| |
|
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
|
 |
 |
Wannan Kundi na Afirka, yana nufin akida ce mai girma, ta tsarin ka'idodin zamantakewar tare, wanda kuma jagora ne ga kungiyoyin gwagwarmayar neman ci gaba da suke Afirka; wadanda suka hada kai don mantawa da bambance-bambancen da ke tsakaninmu, tare da neman tattara dabaru, da hikimomi da kuma ilmi. Kuma shi wannan Kundi na Afirka, ginshiki ne da zai hade abubuwan da muka dauka da matukar muhimmanci na daga manufofinmu da abin da muka sa a gaba, wanda zai zama babban tushe na samun tsararren hadin kai a Afirka na kungiyance, domin samun damar ‘yantar da kai daga dukkan danniya.
|
|
"Kabila ta mutane kamar dan Adam ta ke; sai in har ta yi amfani da gwanintarta, ta kuma rungumi yin takama da tarihinta, kuma ta tashi haikan don kare tsarin rayuwarta, haka kuma idan ba ta tashi don tabbatar da 'yancinta ba, to har abada zai yi wahala (wannan kabila) ta cimma burinta na rayuwa”.
- El Hajj Malik Shabazz |
|
 |
 |
Wannan tsarin dokoki na Kundin Afirka, hanyoyi ne da a ka yarda da su domin magance matsalolin halin da muke ciki a duniyar nan.Tubali na farko, a wannan Kundi, shi ne samin abin kwatanci da za mu yi aiki da shi, don rage sabani tsakaninmu, mu kuma tabbatar cewa mun yi amfani da dumbin albarkatunmu [na kasashen Afirka] ta bangarori ma su ma'ana da za su amfanar da mu. Hakika, wannan zai ba da dama bayyananniya mai kuma tushe, wanda za ta amfanar da kusoshi na ka'idodi guda bakwai (7) watau; adalci, da yunkurin neman ‘yancin kai da hadin kai, da tsarin rayuwa, ilmi, [zamantakewar] iyali da kuma tattalin arziki.
|
|
Ba abin da yake bayyana halin da muke ciki a yau a Afirka, na gama gari face tarihi na zalunci, maimakon tsarin manufar rayuwa bai daya. Domin a wurin tabbatar da ra'ayoyinmu da muke so kwarai, babu hadin kai, wannan shi ya kawo rashin samun tushe na hadin kai da zai amfanar da mu.
Yaudaran kanmu ne da bata lokaci, idan muka ci gaba da yunkurin hadin kai karkashin wariyar launin fata. Abin da kawai zai taimaka mana shi ne hadin kai karkashin akida mai kyau. Don haka, wannan Kundi na Afirka ya tsamo hanyoyin mantawa da bambance-bambancenmu a matsayin jinsi guda; don kuwa ko Musulmi ne, yaren Igbo, Kirista ne ko Bayahude, mai bautar Ubangiji, mutumin yankin Karebbiyan ne [watau Caribbean], Balarabe ne ko mutumin Amirka, duk za mu iya haduwa kan abin da zai amfanar da rayuwarmu gaba daya. |
|
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
 |
|